Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kwalejin horas da manyan hafsoshin sojin Najeriya ta kori hafsoshi biyu bisa zargin sata

Published

on

Kwalejin horas da manyan hafsoshin soji dake Jaji a jihar Kaduna ta kori wasu manyan jami’an soji biyu bisa zargin sata.

Jami’an da lamarin ya shafa su ne Maj I Abdullahi (N/12034) da Lt Cdr MI Madume (NN/2938).

Kwalejin ta Jajin cibiya ce ta horaswa da aka kafa don Sojojin Najeriya, da suka hadar da sojoji, sojojin sama da na ruwa don samar da manyan kwararrun hafsoshin soja.

Wata majiya ta fadawa Solacebase a daren ranar Lahadi 4 ga watan Yuli cewa, an kori Maj I Abdullahi mai lamba (N/12034) sakamakon satar wayar hannu, yayin da Lt Cdr MI Madume mai lamba (NN/2938) aka kore shi saboda satar kudi naira N250,000.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!