ilimi
Kwalejin Noma ta Dambatta na iya cin gajiyar tallafi daga Kanada- SSANIP

Kungiyar manyan ma’aikatan kwalejin kimiyya da fasaha ta SSANIP ta yaba wa gwamnatin jihar Kano bisa irin kokarin da ta ke yi wajen ciyar da ilimi gaba.
Shugaban kungiyar na Najeriya Kwamared Phillip Ogunsupe, ne ya bayyana hakan yayin taron shugabannin kungiyar na ƙasa karo na 77 da aka gudana a Kwalejin Noma ta Audu Bako dake Dambatta, a Kano.
Kwamared Phillip Ogunsupe, ya ce jihar Kano na fitar da kudi wajen yin ayyuka a fannin ilimi, a don haka yake bukatar sauran jihohi da su yi koyi da abin da jihar Kanon Ke yi.
Ya kuma bayyana cewa kwalejin Noma ta Dambatta na iya cin gajiyar wani shiri na haɗin gwiwa da Olds College of Agriculture and Technology, Alberta, da ke Kanada.
Ya ce wannan zai taimaka wajen binciken, horas da malamai a tsakanin cibiyoyin.
Da yake jawabi shugaban kwalejin Noma ta Danbatta, Farfesa Muhammad Wailare, wanda mataimakinsa Dakta Hassan Ibrahim ya wakilta, godewa gwamnatin Kano ya yi da dukkan wadan da suka bayar da gudunmawa wajen gudanar da taron.
Yayin taron dai an tattauna yadda za a samar da ci gaban da ya kamata a kwalejojin Ilimi na Polytechnic da samar da walwala da jin dadin malamai
You must be logged in to post a comment Login