Labarai
Kwamishina a Kano ya yi murabus sakamakon rikicin siyasa

Kwamishinan Kimiyya, Fasaha da Kirkire-kirkire na Jihar Kano, Yusuf Ibrahim Kofarmata, ya yi murabus daga mukaminsa nan take, yana danganta matakin da yanayin rikicin siyasa da ke gudana a jihar.
A cikin wasikar murabus dinsa, Kofarmata ya ce yanayin siyasar da ke cike da matsin lamba da tsammanin biyayya na iya kawo shakku kan ‘yancin yanke hukunci da tsarkin aikinsa a matsayin kwamishina, abin da ya ce bai dace da ka’idojin aiki na gwamnati ba.
Ya ce ya dauki matakin ne domin kare martabar mukamin da kuma amincewar jama’a, inda ya gode wa Gwamnatin Jihar Kano bisa damar da aka ba shi, yana fatan murabus dinsa zai taimaka wa ma’aikatar ta cigaba da aiki ba tare da tangarda ba
You must be logged in to post a comment Login