Labarai
Kwamishinan ma’aikatar al’adu na Kano ya sauka domin takarar majalisar tarayya
Kwamishinan ma’aikatar al’adu da yawon buɗe idanu na Kano Ibrahim Ahmad Ƙaraye ya sauka daga muƙaminsa don takarar ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Ƙaraye da Rogo.
Mai taimakawa Gwamnan kan kafafen sada zumunta Abubakar Aminu Ibrahim ne ya sanar da hakan ta shafinsa na Facebook.
Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan da Gwamna Ganduje ya bai wa masu riƙe da muƙaman siyasa da ke sha’awar takara umarnin ajiye aiki domin biyayya ga dokar zaɓe.
Kawo yanzu Kwamishinoni huɗu ne suka ajiye muƙamansu a yau, tare da wasu daga hadiman Gwamnati da zimmar tsayawa takara.
You must be logged in to post a comment Login