Connect with us

Labarai

Kwamitin gudanarwar Jam’iyyar APC ta jihar Lagos ta dage zaben fid da gwani

Published

on

Kwamitin gudanarwar jam’iyyar APC na kasa ya da’ge zaben fid da gwani na gwamnan jihar Lagos wanda tun da fari a shirya gudanarwa a yau Litinin.

 

Haka kuma jam’iyyar ta sauya ranar da za a gudanar da zabukan fitar da gwani na gwamna a jihohin Enugu da kuma Adamawa.

 

APCn ta kuma canja tsarin gudanar da zabukan jihohin biyu wato Enugu da Adamawa daga zaben delegate zuwa zabe ‘yar tinke.

 

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa Yekini Nabena.

 

A cewar sakataren yada labaran jam’iyyar ta APC a yanzu, za a gudanar da zaben fid da gwani na gwamnan jihar Lagos ne a gobe Talata, yayin da a ranar Alhamis hudu ga wata za a gudanar da na jihohin Enugu da Adamawa.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 341,025 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!