Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ministar harkokin mata Aisha Jummai Alhassan ta yi murabus daga mukamin ta

Published

on

Ministar harkokin mata Sanata Aisha Jummai Alhassan ta yi murabus daga mukamin ta, sannan ta fice daga jam’iyyar APC.

Ta ce ta yi murabus ne tare da kuma ficewa daga jam’iyyar APC, biyo bayan haramta ma ta tsayawa takarar gwamnan jihar Taraba da kwamitin gudanarwar jam’iyyar APC ya yi a baya-bayan nan.

Ta ce haka kawai zikau aka haramta ma ta takarar ba tare da wani cikakken hujja ba.

Sanata Aisha Jummai Alhassan ta kuma ce idan har ba ta cancanta ta tsaya takarar gwamna ba, to kuwa a ganin ta, ba ta cancanci ta ci gaba da kasancewa a matsayin minista kuma ‘yar jam’iyyar APC ba.

Ta kuma godewa shugaban kasa Muhammadu Buhari da shugabannin jam’iyyar APC a mazabar ta da sauran mambobin jam’iyyar sakamakon damar da suka ba ta na kasancewa minista.

A shekaran jiya Alhamis ne kwamitin tantance ‘yan takara na jam’iyyar APC, ya haramtawa Sanata Aisha Jummai Alhassan da ministan sadarwa Adebayo Shittu daga tsayawa takara a zaben fidda gwani na ‘yan takarar gwamnoni da jam’iyyar za ta gudanar a gobe Lahadi.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!