Labarai
Kwara: An tura karin Yan Sanda yankin Kaiama domin karfafa tsaro da zaman lafiya

Rundunar ’yan sandan Jihar Kwara ta tura karin jami’an tsaro zuwa yankin Kaiama domin karfafa tsaro da tabbatar da lafiyar mazauna yankin da matafiya bayan fashewar Bam.
Hakan na cikin sanarwar da Jami’ar Hulda da Jama’a ta rundunar ’yan sandan jihar SP Adetoun Ejire Adeyemi ta fitar a jiya Litinin.
Sanarwar ta bayyana cewa an dauki matakin ne bayan fashewar bam a yankin, inda aka kara kaimi wajen sa ido da sintiri domin dakile duk wata barazana.
Haka kuma, rundunar ta bukaci al’umma da su kasance masu bin doka tare da kai rahoton duk wani abu da ba su gamsu da shi ba ga jami’an tsaro domin daukar matakin da ya dace.
You must be logged in to post a comment Login