Labarai
Kwastam ta rage lokacin fitar da kaya daga kwanaki 21 zuwa awa 48

Hukumar Kwastam ta Najeriya ta kaddamar da sabon tsarin One-Stop-Shop domin rage lokacin fitar da kaya daga kwastam daga kwanaki 21 zuwa awanni 48 kacal.
An kaddamar da shirin ne ranar Alhamis, 23 ga Satumba, 2025 a taron shugabannin hukumar da aka gudanar a Abuja, karkashin jagorancin shugaban kwastam na kasa, Adewale Adeniyi.
Adeniyi ya bayyana shirin a matsayin sauyi na zamani da ya dace da manufofin gwamnatin tarayya na sauƙaƙa harkokin kasuwanci. Ya ce tsarin zai kawar da maimaita bincike, ya tsabtace ayyuka, ya kara gaskiya, tare da dawo da kwarin gwiwar ‘yan kasuwa.
A karkashin tsarin, dukkan sassan kwastam za su yi aiki tare a wuri guda kan takardun da aka samu matsala, don guje wa jinkiri. Ana kuma sa ran kayan da aka kammala bincike a karkashin wannan tsari ba za su sake fuskantar tsaiko ko karin bincike ba.
Shirin zai fara aiki a tashoshin ruwa na Apapa, Tin Can Island da Onne, kafin daga baya a shimfida shi a fadin kasar.
Shugaban kwastam ya jaddada cewa shirin ya yi daidai da sabuwar dokar NCS ta 2023, kuma ya dace da yarjejeniyar saukaka cinikayya ta hukumar WTO.
Shugabannin kwastam na jihohi sun yaba da shirin, suna mai cewa ya dace kuma lokaci ya yi da ya kamata a aiwatar da shi don kara ingancin aiki a hukumar.
You must be logged in to post a comment Login