Connect with us

Labarai

Labari mai dadi : Za a ci gaba da jigilar jirage zuwa kasashen ketare

Published

on

Gwamnatin tarraya ta ce daga ranar 29 ga wannan watan na Agusta zata fara jigilar jiragen sama na kasashen waje tun bayan da ta dakatar da shi a ya yin da aka sami bullar cutar COVID-19.

Ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika ne ya sanar da hakan a shafin sa na Twitter inda y ace, gwamnati ta yanke shawarar ne a ya yin da take karbar rahoton kwamitin yaki da cutar Corona na fadar shugaban kasa.

Amma kuma ministan yace, hanyoyin da aka bi wajen dawo da jigilar zai yi daidai da na lokacin da aka dawo da jigilar jiragen na cikin gida

Har ila yau yace za a fara ne a ranar Asabar mai zuwa ta filin jirgin saman Murtala Muhammad dake Legas da kuma na Nnamdi Azikiwe dake babban birnin tarayya Abuja.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!