Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Lagos:mutane da dama sun rasa rayukansu a wata gobara

Published

on

Ana zaton mutane da dama sun rasa rayukansu sakamakon wata gobara da ta tashi a wata tashar mota da ke Unguwar Ijegun a Lagos da safiyar yau Alhamis.

 

Rahotanni sun ce ana zargin batagari ne da ke fasa bututun mai su ka yi sanadiyar tashin gobarar, bayan da daya daga cikin tankokin da su ka yi satar mai da shi ya yi hatsari ya kuma kama da wuta.

 

Wasu shaidun gani da ido sun shaidawa manema labarai cewa, bayan da tankar man ta fadi ta kama da wuta, jama’ar yankin sun tsere domin tsira da rayukansu.

 

Sai dai Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Lagos (LASEMA) ta cikin wata sanarwa da ta fitar dazun nan, ta ce, ya zuwa yanzu, ta gano gawawwakin mutane biyu, sannan kuma motoci talatin sun kone kurmus.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!