Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Lagos:Tankar man fetur da ta kama da wuta tayi sanadiyar konewar motoci 7

Published

on

Da Asubahin yau ne wata Tanka makare da Man Fetur ta kama da wuta a kan titin Badagry tsakanin Barikin Soja na Onireke da ke karamar hukumar Ojo a Jihar Lagos, tare da kone Motoci 7 kurmus.

Wutar ta fara ci tun karfe 5 na asuba inda ta kone Mota kirar Fijo da Hummer Jeep da wasu Motocin safa-safa guda biyu da wasu manyan Motoci uku.

Wani jami’in hukumar kiyaye aukuwar hadura ta kasa FRSC da ya halarci wurin ya shaida cewa babu asarar rai sai dai ta dukiya mai dimbin yawa.

Shaidun gani da ido sun bayyanawa manema labarai cewa sun hango mutanen cikin Motocin na gudun tsira a dai dai lokacin da al’amarin ya faru don ceton kai, ciki har da Mata.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!