Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Shugaban Jam’iyyar APC ya ce babu wata tangarda a zaben fidda gwani na jihar Lagos

Published

on

Shugaban jam’iyyar APC mai mulkin kasa Adams Oshimhole ya shaidawa shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa zaben fidda gwani na gwamna a Jihar Lagos ya gudana daidai babu wata tangarda.

Adams Oshimhole na fadin hakan lokacin wata ganawa da shugaban kasa a fadarsa dake Villa, inda ya ce zaben fidda gwanin ya gudana cikin kwanciyar hankali da lumana.

Sai dai jagoran kwamitin gudanarwar APC da ya sanya ido kan zaben Clement Ebri ya ce akwai kura-kurai cikin zaben matuka, a don haka ne suka nuna rashin amincewarsu da sakamakon zaben.

Shi kuwa shugaban APC na Jihar ta Lagos Tunde Balogun watsi ya yi da rahoton Kwamitin yana mai cewa an yi zabe lafiya bisa gaskiya da adalci.

Jagororin APCn da suka halarci zaben dai sun hadar da Bola Ahmad Tinubu da mataimakiyar gwamna Idayat Adebule da shugaban Majalisar Dokokin Jihar Mudashiru Obasa da mai neman takarar gwamnan Babajide Sanwa-Olu.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!