Labarai
Laifin Almundahana: Sarkin Kano ya cire mai unguwar Ƙofar Ruwa B
Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya cire mai unguwar Ƙofar Ruwa B Malam Haruna Uba Sulaiman daga matsayinsa.
Mai martaba sarkin ya tube mai unguwar ne bisa samunsa da laifin yin zamba cikin aminci a unguwar ta Ƙofar ruwa.
Malam Haruna Sulaiman Uba an same shi da laifin sayarwa wata mata wani kudiddifi wanda ba mallakin sa ba.
Kudiddifin dai mallakin masarautar jihar Kano ne.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayar da umarnin cire Mai unguwar ne nan take ba tare da ya ci gaba da gudanar da mulkin jama’ar unguwar ba.
Da yake bayani wakilin Arewa Faruq Muhammad Yola ya ce, dama ba wannan ne na farko da aka taɓa kama shi da laifin cin amana da almundaha ba.
Har ma ya ce “Sarki ya umarci hakimin ƙaramar hukumar Dala ya kawo wani domin a naɗashi a matsayin Sabon Mai unguwar.
You must be logged in to post a comment Login