Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

ilimi

Lambar katin ɗan kasa zai zama wajibi a lokacin rijistar jarrabawa – WAEC

Published

on

Hukumar shirya jarrabawar kammala sakandire ta yammacin Afrika WAEC ta ce, za ta sanya buƙatar lambar katin ɗan ƙasa ta NIN ya zama wajibi ga ɗaliban da za su rubuta jarrabawar a ƙasar nan.

Mai magana da yawun hukumar Patrick Areghan ne ya bayyana hakan, yayin da yake jawabi a jihar Lagos.

Ya ce, hukuncin hakan ya biyo bayan dokar da gwamnatin tarayya ta sanya na buƙatar mallakar katin zama ɗan kasa ga kowanne ɗan kasar nan.

Patrick ya kuma ce, tuni hukumar ta buƙaci ɗaliban da za su rubuta jarrabawar a bana, da su mika lambar NIN ɗin su ga hukumomin makarantar.

Hukumar ta ce, daga shekarar 2022, sanya lambar NIN ɗin yayin yin rijistar jarrabawar zai zama wajibi ga kowane dalibi.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!