Kiwon Lafiya
Ma’aikatan hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa NEMA sun fara yajin aikin gama gari
Ma’aikatan hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa NEMA sun fara yajin aikin gama gari, wadanda suka ce sun yi hakan ne don nuna adawa da rashin iya jagorancin shugaban hukumar Mustapha MaiHajja.
Jagoran ma’aikatar ta NEMA Justine Uche, yayin wani taron manema labarai a Abuja, ya ce; tun kama aikin Mustapha Maihajja a watan Afrilun shekarar da ta wuce lamura suka tabarbare a hukumar.
A cewar sa ba za su dawo bakin aiki ba har sai an samu kyautatuwar lamura a hukumar.
Justine Uche, ya kuma ce a yanzu kusan komai ba ya wakana kamar yadda yakamata, musamman asibitocin tafi da gidanka da ke ba da agajin gaggawa ga wadanda suka samu munanan raunuka da motocin ba da agaji da kuma shalkwabta wanda gwamnati ta kashe dala miliyan dari wajen sayan sa.
Ma’aikatan dai sun yi ta daga kwalaye mai dauke da rubuce-rubuce ba mason Maihajja, Maihajja annoba ne