Connect with us

Coronavirus

Ma’aikatan lafiya 7 sun kamu da Coronavirus a Borno

Published

on

Gwamnatin jihar Borno ta ce jami’an lafiya 7 ne suka kamu da cutar Covid-19 a jihar.

Kwamishinan lafiya na jihar kuma sakataren kwamitin yaki da cutar Covid-19 na jihar Salihu Kwaya-Bura ne ya bayyana hakan a ranar jumu’ar nan, yayin taron bayar da bayanai kan halin da ake ciki game da annobar a jihar.

Jaridar Premium Times ta rawaito kwamishinan ya ce yanzu haka an samu mutum 15 da suka kamu da cutar, inda 2 daga ciki suka rasu.

Sannan yanzu haka an killace mutane 145 wadanda sukayi mu’amala da wadanda suka kamu da cutar domin tabbatar da lafiyarsu.

Har ila yau kwamishinan ya ce baya ga wadancan, sun samu kira har guda 9 daga al’ummar gari wanda yanzu haka suke kan bincike akai.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!