Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ma’aikatan sashin shirye-shirye na Freedom Radiyo sun karrama Aisha Bello Mahmud

Published

on

Ma’aikatan sashin shirye-shirye sun karrama shugabar sashin Hajiya Aisha Bello Mahmud.

Tawagar ma’aikatan sun karrama ta da yammacin ranar Litinin sakamakon yadda ta ke kula da su da kuma ƙoƙarin ciyar da su gaba

Guda daga cikin ma’aikatan sashin Samira Sa’ad Zakirai da ta wakilci sauran ta ce “Mun karrama shugabar mu ne bisa yadda take jajircewa wajen nuna yadda aiki yake da kuma ba mu shawarwari masu kyau, baya ga ƙoƙarin ciyar da mu gaba”.

“Mun lura babu abinda za mu yi mata mu nuna godiyar mu face mu karramata da wani abu da zai faranta mata rai, kuma ta riƙa tuna godiyar mu gare ta, domin ta cancanci mu bata lambar girmamawa” a cewar Samira.

Da yake miƙa kyautar ga Hajiya Aisha Bello Mahmud, shugaban tashar Freedom Radio Malam Ado Sa’idu Warawa ya yaba mata kan jajircewarta akan ayyukan ta musamman yadda ta riƙe sashin tsawon shekara biyar ba tare da samun tangarɗa ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!