Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Magidanci ya saduda ba yanda ya ga sunan Allah a jikin Doya

Published

on

Wani magidanci da ke karyata ganin sunan Allah da ke fitowa a jikin wasu abubuwa da dama, ya saduda bayan da sunan Allah subhanahu wata’ala ya fito baro-baro a jikin wata doya da ya saya.

Magidancin mai suna Usman Jibrin Gabi mazaunin unguwar Janbulo a nan Kano, ya bayyana hakan ne yayin tattaunawarsa da Freedom Radio a karshen makon da ya gabata.

Ya ce, a baya dai ya sha karyata labaran faruwar ganin Dabbobi da wasu abubuwa da dama da aka ce an gani dauke da sunan Allah subhanahu wata’ala ko kuma na Manzon Allah Salallahu alaihi wasallam.

Sai dai kwatsam bayan da ya siyo wata Doya daga Zuba dake garin Abuja inda ya kawo ta nan Kano, kuma matarsa tana yankawa da zummar yin amfani da ita sai ga sunan Allahu ya fito baro-baro a jikin doyar.

Kazalika Magidancin ya kara da cewa, lokacin da ya ga sunan ya cika da farinciki, kasancewar ya sha karyata faruwar lamarin a baya, inda nan take ya sanar da mahaifinsa faruwar lamarin.

Da take tabbatar da faruwar lamarin, matar magidancin Samira Aliko Mai shanu, ta bayyana cewa maigidan nata ne ya ankarar da ita rubutun kasancewar kwana biyu da yanka doyar.

Haka kuma ta kara da cewa bayan faruwr lamarin ne sai ta sanar da mahaifiyarta ta wayar tarho kan lamarin ganin sunan, inda ta bayyana mata cewa su yi gaggawar cinye doyar domin tana dauke da albarka inda nan take ta soya ta tare da kwai suka yi kalaci.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!