Labarai
Majalisa ta bukaci hukuncin shekara 5 a gidan yari ga duk malamin da aka kama da cin zarafi
Majlisar dattijai ta Najeriya na sake ziyararta kudirin da zauren majalisa ta takwas tayi na hukunta masu yunkurin masu aikata yin fyade.
Zauren majalisar ta takwas ta nemi daure wadanda suka yi yunkurin fyaden da shekaru biyar a gidan kaso , yayin data bukaci cin tarar naira miliyan biyar ga malaman jami’o’i da aka kama da yunkurin yi wa dalibai mata fyade da cin zarafin dalibai maza.
Koda yake tabbatar da kudirin dokar ya samu jinkiri sakamakon samun nazari daga bangaren shugaban kasa, bayan zaman zauren majalisar.
Mataimakin shugaban majalisar ta kasa Sanata Ovie omo-Agege ne dai ya gabatar da kudirin a zaman majalisar na jiya laraba.
Kamar yadda kudirin ya bayyana ,yana mai cewa ‘dokar ta ce dukkanin malamin da yayi yunkuri cin zarafin dalibi ko daliba da suke kasa da shekaru 18 ba da son ransu ba a matsayin wata hanya da zai ci jarabawa ko samar da wata dama a harkokin karatu, to lallai wannan malami ya aikata laifi.
A wata sanarwa da mai bada shawara akan harkokin sadarwa Yomi Odunuga ya fitar ya ce sanata Omo-Agege ya bukaci yan Najeriya da su marawa kudirin baya.
Ya kuma yabawa Aisha Buhari da Bisi Fayemi da kungiyar malamai ta kasa da dukkanin wadanda suka baiwa tashar BBC bayan wajen taimaka musu fito da matsalolin cin zarafin dalibai da