Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yadda aka tsige mataimakin shugaban majalisa a Kaduna

Published

on

Majalisar Dokokin jihar Kaduna ta Amince da tsige mataimakin shugaban majalisar daga kan mukamin sa, Mukhtar Isaha Hazo, wanda ke wakiltar Basawa a karamar hukumar Sabongari, bisa zarginsa da hada baki da wasu daga cikin ‘yan majalisar 21 don tsige shugaban majalisar Yusuf Ibrahim Zailani wanda yake son maye gurbinsa a shugaban majalisar.

Rahotonni sun bayyana cewa yan majalisa 21 sun shirya da zarar sun zo majalisar zasu kawo kudirin tsige shugaban majalisar, inda shi kuma shugaban majalisar da ya samu labari ya shirya zaman gaggawa a yau domin tsige mataimakin na sa.

Wakilin Freedom Radio a can jihar ta Kaduna Babangida Aliyu Abdullahi ya rawaito cewa kafin tsige mataimakin shugaban majalisar da misalin karfe daya na rana mambobin majalisar sun gudanar da wani zaman sirri a tsakanin su.

Zaman majalisar ya samu halartar ‘yan majalisa 25 inda suka amince da a tsige mataimakin shugaban majalisar bisa aikata zamba cikin aminci da cin amana da ake zargin sa da yi.

Zulum ya tabbatar da mutuwar mutane 81 da ‘yan ta’adda suka kaiwa hari

Abuja ta zarce Kano yawan masu Coronavirus

Kafin zauran majalisar ya Amince da cire mataimakin shugaban majalisar an samu rikici tsakanin mambobin ta inda wasu suka amince da a tsige shi wasu kuma suka nuna rashin goyon bayan su.

Yayin zaman a yau tubabben mataimakin shugaban majalisar Mukhtar Isah Hazo yayi kokarin sace sandan majalisar wanda wasu daga cikin ‘yan majalisar suka dakatar da yunkurin nasa na fita da sandan majalisar.

Yanzu haka dai ta tabbata Mukhtar Isah Hazo ya rasa kujerar sa ta mataimakin shugaban majalisar inda zai ci gaba da wakilitar karamar hukumar sa da yake wakilta ta Basawa dake sabon gari a jihar ta Kaduna.

Rahotonni sunyi nuni da cewa bayan tsige mataimakin shugaban majalisar da mambobin majalisar su kayi, kowanne daga cikin ‘yan majalisar ya fice daga zauren majalisar ba tare da zantawa da manema labarai game da jin karin bayani kan tsige mataimakin shugaban majalisar ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!