Connect with us

Labarai

Majalisar Dattawa da gwamna Zulum sun bukaci Tinubu ya ɗauki matakin gaggawa a fannin tsaro

Published

on

Majalisar Dattawa hadi da gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, sun bukaci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya ɗauki matakin gaggawa kan hare-haren ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas.

 

A wata tattaunawa da Gwamna Zulum yayi da gidan talabijin na News Central ya shawarci Shugaban Ƙasa da ya mayar da hankali kan shawarwarin da ƙwararrun jami’an tsaro suke bayarwa,maimakon masu faɗa a ji na siyasa, musamman a yaki da ‘yan ta’addan Boko Haram.

 

Hakazalika, Majalisar Dattawa, ta nemi daukar matakin haɗin gwiwa tare da bada shawarar kafa sansanin soji a karamar hukumar Hong da ke Jihar Adamawa.

 

Zulum ya kara da cewa mafita ga wannan rikicin tsaro da ya dade yana addabar yankin,shi ne barin masu ido a bangaren tsaro su yi abunda ya kamata  da kuma ajiye siyasa a harkar.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!