Connect with us

Labarai

Majalisar Dattawa ta fara nazari kan ƙudirin gyaran dokar zaɓe

Published

on

Majalisar dattawa ta fara nazari kan ƙudirin gyara dokar zaɓen shekara ta 2022, inda ta mayar da hankali kan wasu sassa da ake ganin suna buƙatar ƙarin gyara domin inganta zaɓe a ƙasar nan.

 

Ƴan majalisar sun yi hakan ne ta hanyar fara nazarin wasu takardu da gyare-gyaren da shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin Zaɓe, Sanata Simon Lalong, ya gabatar, kafin a ci gaba da muhawara a bainar jama’a.

 

Ƙudirin ya ƙunshi batutuwa kamar hana yin rajista a jam’iyyun siyasa fiye da ɗaya da daƙile sauya sheƙa bayan zaɓen fidda gwanida  da kuma tanadin hukunci ga masu karya doka.

 

A zaman majalisar na yau Alhamis, ‘yan majalisar sun amince da buƙatar janye wasu sassan ƙudirin da aka riga aka amince da su a watan Disambar 2025, domin a sake duba su.

 

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya jaddada muhimmancin yin nazari mai zurfi kan ƙudirin, duk da cewa Majalisar Wakilai ta riga ta amince da shi, yana mai cewa, dokar na da matuƙar muhimmanci musamman yayin da ake shirin zaɓen shekara ta 2027, don haka kamata ya yi, a yi taka-tsantsan domin kauce wa rikice-rikicen shari’a bayan zaɓe.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!