Labarai
Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da naɗin Janar Christopher Musa a matsayin sabon ministan tsaro

Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da naɗin Janar Christopher Musa a matsayin sabon ministan tsaro.
Zaman majalisar ya cika da ruɗani a yau Laraba yayin da wasu ‘yanmajalisar ke cewa janar ɗin, wanda shi ne tsohon babban hafsan tsaron Najeriya, ya rusuna ya wuce ba tare da amsa tambayoyi masu yawa ba, da kuma waɗanda suka ce dole sai ya amsa.
Daga ƙarshe dai Shugaban Majalisa Godswill Akpabio ya shawo kan hayaniyar kuma ya amince cewa akwai buƙatar Janar Musa mai ritaya ya amsa tambayoyin da suka dace.
Da yake jawabi, janar ɗin ya bayyana shirinsa na shawo kan matsalar tsaro, da kuma dawo da martabar rundunar sojin ƙasar a idon ‘yan Najeriya.
Ana sa ran Janar Musa zai fara aiki nan take bayan Mohammed Badaru ya sauka daga muƙamin a ranar Litinin.
You must be logged in to post a comment Login