Labarai
Majalisar dattijai ta kawo kudirin zamantar da illimin tsangaya
Majalisar dattijan kasar nan ta bukaci gwamnatin tarayya ta zamanantar da manhajar karatun tsangaya irin ta zamani duba da yadda yawan barace-barace ya yawaita a gari a wani yunkurin rage barace baracen akan tituna.
Majalisar dai ta bukaci gwamnatin tarayya da na jihohi da su samar da cibiyoyin koyar da sana’oin dogaro da kai don baiwa almajirai hanyoyin samar da kudaden shiga don daukewa kansu bukatun yau da kullum.
Majalisar ta dauki wannan mataki ne bayan wani kudi da sanata Abdullahi Sankara na jamiyyar APC da ke wakiltar Arewa maso yammancin jihar Jigawa da wasu yan majalisar su 26 da suke marawa baya.
Da yake gabatar da kudirin, sanata Sankara ya nuna damuwarsa ga yadda bara ta yawaita mussamam a manyan tituna da ke fadin kasar nan.
Ya kara da cewa matsalar bara ta zama abin damuwa ga manyan birane da ke Najeriya ,musamman a tashoshin motoci, da wuraren addinai , kan tituna , wuraren bukukuwa da sauran inda al’umma ke taruwa.
Sanata ya ce matsalar bara bai alakantu da wani sashe na kasar nan ba hasali ma ya na nuna mummunar misali ne ga idon duniya, da kuma kasar baki daya , wanda ake yi musu kallon wasu daga cikin su kan fada kungiyoyin yan tada kayar baya.