Labarai
Za mu samar da hukumar hana barace-barace a Kano – Ganduje
Gwamnatin jihar Kano ta ce, za ta samar da wata hukuma da za ta riƙa hana ayyukan barace-barace a jihar Kano.
Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan a ranar Talata lokacin da ya karɓi bakuncin gamayyar ƙungiyoyin ci gaban al’umma.
Ganduje ya ce “Ba za mu zuba ido ƙananan yara suna barace-barace a kan titi ba, kuma ba sa zuwa makaranta duk da cewa ilimi kyauta ne kuma dole a jihar Kano”.
“A don haka za mu samar da hukuma da za ta kula da ayyukan barace-barace don tabbatar da cewa kowanne yaro yana zuwa makaranta, don samar da ingantacciyar rayuwa”.
Gamayyar kungiyoyin dai sun kai wa gwamna Ganduje ziyara kan takardar da suka gabatar da ke buƙatar ɗabbaƙa dokar 2013 da ta hana barace-barace a titunan Kano, ƙarƙashin shugaban Kwamared Ibrahim Wayya.
Gamayyar ƙungiyoyin sun kai ziyarar yayin zaman majalisar zartarwa.
Wayya ya ce “Magance barace-baracen zai taimaka Gaya wajen bai wa yara damar samun ilimi”.
A zaman majalisar zartarwar, wani kamfani ya gabatar da buƙatar sahalewar gwamnatin wajen yin aikin samar da wuta mai amfani da hasken rana wato solar musamman a yankunan karkara.
You must be logged in to post a comment Login