Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Majalisar dattijai zata tantance Manjo Janar Bashir Salihi da Timpire Sylva yau

Published

on

Shugaban majalisar dattijai Sanata Ahmad Lawan ya bayyana cewa a yau ne majalisar za ta tantance Manjo Janar Bashir Salihi Magashi daga nan Kano da Timipre Sylva daga Bayelsa, don dorawa akan guda 10 da ta tantance a jiya Talata.

Sauran wadanda za a tantance a yau din sun hada da Richard Adeniyi Adebayo daga Ekiti da Mustapha Baba Shehuri daga Borno da Ramatu Tijjani daga Kogi sai Muhammad Abdullahi daga Jihar Nasarawa.

Har ila yau akwai Tayo Alasoadura daga Ondo da kuma Sunday Dare daga Oyo.

A jiya dai majalisar ta tantance ministoci 10 a cikin tsawon sama da sa’o’i 6, inda ta baiwa guda 6 daga cikinsu kulawa ta musamman bayan da ta ce su yi gaisuwar nan ta al’ada su wuce, kasancewarsu tsoffin ‘yan majalisa.

Guda goman da aka tantance jiyan sune Sanata Godswill Akpabio daga jihar Akwa Ibom da Rotimi Amaechi daga Rivers da Uchechukwu Ogah daga Abia, sai George Akume daga Benue.

Sauran su ne Ogbonnaya Onu daga Ebonyi da Emeka Nwajiuba daga Imo da Olurunimbe Mamora daga Lagos, sai Olamilekan Adegbite daga Ogun da Adamu Adamu daga Bauchi da kuma Sharon Ikeazor daga Anambra

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!