Labarai
Majalisar dokoki ta fara tantance sabbin kwamishinoni
Majalisar dokokin jihar Kano ta fara tantance sunayen sabbin kwamishinonin da ake son nadawa.
Majalisar ta sake karɓar sunan tsohon kwamishinan lafiya Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa domin sake tantancewa a matsayin kwamishina.
Tun da fari dai gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ne ya aikewa majalisar da sunansa domin tantancewa tare da sahalewa don a sake naɗa shi a matsayin kwamishina.
Shugaban majalisar Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari ne ya sanar da hakan ta cikin wasiƙar da gwamnan ya aike, wadda kuma ya karanta ta a zaman majalisar na ranar Litinin.
Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da yanzu haka mutane takwas da gwamnan ya aike wa majalisar suka halarci zauren domin tantance su.
Wakilinmu Freedom Radio Auwal Hassan Fagge ya, ya ruwaito cewa majalisar ta amince a kirawo Dakta Ali Musa Hamza Burum-Burum da kuma Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa domin su ma a tantance su a yau.
Majalisar ta fara tantancewar ne da tsohon shugaban majalisar dokokin ta Kano Alhaji Ya’u Abdullahi Yanshana, da kuma Dakta Ali Musa Burum-Burum.
Yanzu haka dai majalisar na ci gaba da tantance sauran mutane uku.
You must be logged in to post a comment Login