Labarai
Majalisar dokoki za ta yiwa dokokin kasuwannin Sabon Gari da Singa garambawul
Majalisar dokoki ta jihar Kano, ta amince da dawo da dokokin gudanarwar kasuwannin Muhammadu Abubakar Rimi da Singa.
Dawo da dokokin zai bada dama domin yi musu gyare-gyare.
Amincewar hakan ta biyo bayan Buƙatar da ɗan majalisar mai wakiltar ƙaramar hukumar Dambatta Alhaji Murtala Musa Kore ya gabatar yayin zaman majalisar na ranar Litinin.
Ɗan majalisar na Dambatta ya ce, bayan fara aiki da dokokin akwai wasu matsaloli da suka gano don haka akwai Buƙatar yi musu gyara.
Alhaji Murtala Musa Kore, ya ce akwai sassan dokokin da ya kamata a yiwa gyrae-gyare domin dacewa da irin tanade-tanaden da gwamnatin jihar Kano da kuma ƴan kasuwar suka cimma matsaya a baya.
Haka kuma ya ƙara da cewa, ƴan kasuwar sun samu saɓani da ma’aikatan tattara harajin ƙaramar hukuma, wadda har ta kai sai da kwamitinsa na harkokin kasuwanci na majalisar ya shiga tsakani don samar da daidaito.
A nasa ɓangaren shugaban masu rinjaye na majalisar Alhaji Labran Abdul Madari mai wakiltar ƙaramar hukumar Warawa ya goyi bayan dawo da dokokin domin yi musu gyare-gyare kamar yadda ɗan majalisar ya buƙata.
You must be logged in to post a comment Login