Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Kano: Majalisar dokoki zata gudanar da taron jin ra’ayin jama’a ranar 5 ga watan gobe

Published

on

Majalisar dokokin jihar Kano za ta gudanar da taron jin ra’ayin jama’a kan kunshin kasafin kudin badi Wanda gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya gabatar a kwanakin baya.

 

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na majalisar dokokin ta Kano Ali Bala Kofar Kudu ya fitar.

 

Sanarwar ta ruwaito Ali Bala Kofar Kudu na cewa za a gudanar da taron ne domin neman shawarar jama’a kan kunshin kasafin kudin.za’a dai gudanar da taron ne a ranar biyar ga watan Disamba za ayi taron

 

 

Wakilin mu na majalisar dokokin Kano Abdullahi Isah ya ruwaito cewa, kwamitocin majalisar dokokin ta Kano suna ci gaba da ganawa da shugabannin ma’aikatu da hukumomin gwamnati kan kunshin kasafin kudin jihar Kano na badi.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!