Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Gwamnatin kano za ta kafa hukumar cigaban ilimi

Published

on

Majalisar zartaswa ta jihar kano ta amince da kafa hukumar samar da cigaban ilimi a makarantun dake fadin jihar.

kwamishinan yada labarai na jihar kano kwamared Muhammad Garba, ne ya bayyana hakan a wani taro da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar Kano a daren  jiya Litinin.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labaran na jihar Kano kwamared Muhammad Garba, ya raba wa manema labarai a nan Kano.

kwamishinan ya ce kafa hukumar zai sanya a samu sauki wajen samar da kudade tare da yin amfani da su wajen samar da ilimin firamare da sakandari kyauta a kanaanan hukumomin jihar 44.

Haka kuma ya kara da cewa an kirkiri hukumar ne domin kawo cigaba a harkokin ilimi da kuma magance karancin kayan aiki da ake fuskanta.

Mallam Muhammad Garba ya kuma ce, za a samo kudaden tafiyar da hukumar daga kudaden harajin yau da kullum da adadinsu ya kai kaso 5 sai kuma kaso 2 daga kudaden tafiyar da alamuran kananan hukumomi da kuma sauran daidaikun mutane da kungiyoyi masu bada tallafi.

Kwamishinan ya kara da cewa kudaden da aka tara za a rarraba su  ne inda, jami’o’i mallakar jiha za a basu fiye da kaso 17 sai makarantun gaba da sakandire da za a basu kaso fiye da kaso 12 na kudaden  haka ma makarantun sakandari suna da kaso 35,yayin da makarantun firamare za su samu kaso 25 sai kuma makarantun allo da za a rika ware musu kaso 10.

Ta cikin sanarwar an kuma bukaci majalisar dokokin jihar Kano da ta yi gaggawar mayar da kudirin ya zama doka domin ciyar da jihar Kano gaba.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!