Labarai
Majalisar dokokin Kano ta buƙaci a sanya dokar Ta-ɓaci kan kai yara aikatau

Majalisar dokokin jihar Kano ta buƙaci gwamnatin jihar da ta saka dokar ta-ɓaci kan masu kai yara musamman mata aikatau.
Ɗan majalisar dokokin jihar Kano, mai wakiltar ƙaramar hukumar Madobi, Hon. Sulaiman Mukhtar Ishaq, ne yayi wannan kira yayin zaman majalisar na yau Litinin.
Shi ma wakilin Rano Ibrahim Malami Rano, ya nemi gwamnatin Kano da majalisar dokokin da ta kafa kwamiti, kan iftla’in da ya afkawa al’ ummar mazaɓu takwas da yake wakilta sakamakon iska mai karfi da aka samu a yankin.
A dai zaman majalisar na yau, shi ma ɗan majalisar ƙaramar hukumar Dambatta, Murtala Musa Kore, ya buƙaci gwamnatin Kano ta gyara hanyar da ta tashi daga Ofishin ƴan sanda na Dambatta zuwa garin Balloda zuwa shiddar.
You must be logged in to post a comment Login