Labarai
Majalisar Dokokin Kano ta bukaci a gyara wasu hanyoyi a Garun Malam da Garko

Ɗan Majilisar jihar Kano mai wakiltar mazabar Kura da Garun Malam, Zakariya Alhassan, ya buƙaci gwamnatin Kano da ta duba halin da hanyar da ta tashi daga Chiromawa zuwa garun Babba ke ciki.
Ɗan majalisar ya bukaci hakan ne lokacin da ya ke gabatar da kudiri kan halin da hanyar ke ciki a zaman majalisar na yau Litinin.
Zakariya Alhassan, ya bayyana damuwarsa kan yadda hanyar ke baraza na ga rayuwar al’ummar yankunan.
Haka kuma, a dai zaman majalisar shi ma ɗan majalisar Garko, Injiniya Murtala Kadage, ya gabatar da kudurin neman gyaran hanyar garin Tsohuwar Kasuwa a ƙaramar hukumar ta Garko wadda ruwan sama ya lalata.
Kudirin dai ya samu goyon bayan ɗan majalisa mai wakiltar Rano.
You must be logged in to post a comment Login