Labarai
Majalisar dokokin Kano ta bukaci gwamnati ta gyara hanyar garin Doka zuwa Riruwai

Kazalika majalisar ta nemi gwamnati da ta samar da hanyar da ta samu daga kumurya zuwa garin Wudil don bunkasa harkokin noma a yankin.
A yayi zaman majalisar na yau Talata, ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Doguwa, Salisu Ibrahim, shi ne ya gabatar da kudirin gyaran hanyar da aka samar da ita tun lokacin Marigayi Abdullahi Wase da ta haɗa shalkwatar ƙaramar hukumar ta Doguwa, sai dai a shekarar 2014 tsohon Gwamnan Kano Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayar da aikin hanyar da har yanzu ba akai ga kammala ta ba.
A dai zaman na yau, ɗan majalisa mai wakiltar Bunkure, Hafizu Gambo, ya bayyana irin muhimmancin da wannan hanya ke da ita ga al’ummar yankin musamman wajen fitar da kayan gona.
Da yake miƙa nasa kudirin ɗan majalisar Bichi, Shehu Lawan ya bukaci majalisar da ta yi kira ga gwamnati data gina musu gadar garin Kanƙau, dake kan hanyar Bichi dake da tsawon kilomita sha biyu.
You must be logged in to post a comment Login