Labarai
Majalisar dokokin Kano ta yi dokar kafa hukumar da zata Kula da Manyan gine-gine a kano

Majalisar dokokin Kano ta yi dokar kafa hukumar da zata Kula da Manyan gine-gine da kayan more rayuwa a fadin jihar nan.
Kafa dokar ya biyo bayan amincewa da karatu na uku kan kudurin dokar da majalisar tayi a zaman ta na yau Litinin.
Da yake karin bayani akan sabuwar dokar, shugaban masu rinjaye na majalisar Lawan Hussaini Dala ya ce, idan ankafa hukumar, za ta Sanya ido kan yadda kamfanonin waya suke kafa antennar su da yadda suke haka rami a titunan jihar wajen binne manyan wayoyin su.
majalisar tace, hukumar za kuma ta dauki matakin hukunci akan wadanda suke tone hanyoyi a jihar wajen shimfida bututun ruwa domin kaiwa gidaje ko wajen sana’ar su.
You must be logged in to post a comment Login