Labarai
Majalisar dokokin Kano ta yi dokar kafa hukumar kula da Manyan Allunan talla da tsaftace harkar tallace-tallace a kafafan yada labaran Kano

Majalisar dokokin Kano ta yi dokar kafa hukumar kula da Manyan Allunan talla da tsaftace harkar tallace-tallace a kafafan yada labaran Kano, domin Samarwa da gwamnati karin hanyar samun kudin shiga.
Amincewa da kafa dokar ya biyo bayan karatu na uku Kan ƙudurin dokar da majalisar tayi a zaman ta na yau.
Da yake jawabi ga manema labarai, Shugaban masu rinjaye na majalisar Lawan Hussaini Dala ya ce Allunan talla na daga cikin manyan hanyoyin da ƙasashe suke dogara da su wajen samun kuɗin shiga da Kuma tsaftace birane.
Majalisar ta ce hukumar tana Kuma da hurumin kulawa da dukkanin tallukan da ake sakawa a kafafen yada labaran dake Kano musamman akan tallan da bai dace da dabi’a da al’adar bahaushe ba da kuma masu amfani da gurbatacciyar Hausa.
Majalisar ta ce da zarar gwamna Abba Kabir Yusif ya sanyawa dokar hannu, hukumar za ta fara ayyukanta gadan-gadan.
You must be logged in to post a comment Login