Connect with us

Kiwon Lafiya

Majalisar wakilai na binciken kudaden da aka warewa hukumar kashe gobara

Published

on

Majalisar wakilai ta ce zata binciki kudaden da aka warewa hukumar kashe gobara ta kasa a kasafin kudin shekarar 2011 na naira biliyan biyu da miliyan dari takwas.

 

Wannan mataki dai ya biyo bayan kudirin da dan majalisa daga jihar Lagos Ayeola Abayomi ya gabatar gaban zauren majalisar kan bukatar a binciki budadden yayin zaman majalisar na jiya.

 

A cewar sa majalisar ta damu matukan da ta san ina kudaden suka makale, a don haka ya zama dole majalisar ta binciki hukumar kashe gobarar ta kasa domin sanin halin da kudaden ke ciki.

 

Ya kuma ce la’akari da rayukan daka rasa sakamakon hadarin gobara da kuma asarar dukiyoyin masu ya wa, yakamata a binciki halin da hukumar ke cike kuma me suke yi da kudaden da ake basu.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,342 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!