Labarai
Majalisar wakilai ta ɗage ranar komawa daga hutu

Majalisar Wakilai Najeriya, ta ɗage ranar komawa hutu daga 23 ga Satumba zuwa 7 ga Oktoba, duk da cewar kwamitoci za su ci gaba da gudanar da ayyukan su.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanawa da majalisar ta aikewa dukkan ‘yan majalisar, inda ta yi kira da su sake shirye-shiryen su da tsare-tsaren su domin su yi daidai da canjin da aka samu.
Ta cikin sanarwar shugaban Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya ce yana yi ‘yan Najeriya albishir cewa majalisar za ta hanzarta amincewa da dokar gyaran kundin tsarin mulki na 1999.
Mataimakin shugaban majalisar, Benjamin Kalu, wanda shi ne shugaban kwamitin gyara kundin tsarin mulki, ya ce za a gudanar da tsarin cikin haɗin kai da ba kowane ɓangare dama domin tabbatar da cewa kowa ya samu damar shiga cikin lamarin.
You must be logged in to post a comment Login