Labarai
Majalisar wakilai ta buƙaci gwamnatin tarayya ta jingine aiwatar da sabuwar dokar haraji

Majalisar wakilai ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta jingine shirinta na fara aiwatar da sabuwar dokar haraji mai cike da ce-ce-ku-ce da ruɗani, har sai an kammala bincike kan zargin sauya wasu daga cikin dokokin da majalisar ta amince da su.
Ɓangaren marasa rinjaye a majalisar sun bayyana bukatar dakatar da aiwatar da sabuwar dokar haraji domin gudanar da bincike mai inganci, wanda majalisar ta kafa don gano gaskiyar batun.
Wannan kiran ya biyo bayan zargin cewa an sauya wasu sassa na dokokin haraji bayan da majalisar ta amince da su, wanda hakan ya janyo mummunan ruɗani a tsakanin sassan gwamnati.
A halin yanzu, ɗaya daga cikin shugabannin majalisar, ya bayyana cewa akwai bukatar a tabbatar da gaskiyar wannan al’amari kafin a ci gaba da aiwatar da dokar.
Duk da haka, ɓangaren gwamnatin ya nesanta kansa daga zargin, inda ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa sabuwar dokar haraji za ta fara aiki a ranar 1 ga Janairun, 2026 mai kamawa, kuma akwai haɗin kai tsakanin gwamnati da majalisar kan wannan lamari.
You must be logged in to post a comment Login