Labarai
Majalisar wakilai ta yi barazanar kin bayyana a taron gabatar da kasafin badi
Majalisar wakilai ta yi barazanar kin bayyana a taron gabatar da kasafin shekarar 2019, har sai ministan kasafi da tsare-tsare Udoma Udo Udoma ya aike mata takardar ban hakuri.
Mambobin majalisar sun yi barazanar hakan ne yayin zaman ta na Alhamis, bayan da shugaban majalisar Yakubu Dogara ya karanta wasikar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike wa majalisar kan bukatar gabatar da kasafin badi ranar sha 9 ga watan da muke ciki na Disamba.
A jiya Laraba ne rahotanni suka ruwaito ministan tsare-tsaren Udoma Udo Udoma na cewa tsaikon da aka samu wajen gabatar da kasafin shekarar badin na da nasaba da jan kafar da majalisun tarayyar ke yi.
Wannan ne ya sanya dan majalisa Abubakar Adamu na jam’iyyar APC daga jihar Kwara ya gabatar da kudirin gaggawa gaban zauren majalisar da safiyar yau Alhamis, yana mai cewa mambobin majalisar sun bukaci ban hakurin gaggawa nko kuma su ki bayyana a taron gabatar da kasafin.
A cewar sa kalaman ministan wani yunkuri ne na bata kimar majalisun tarayya, lamarin da ya sanya dukkanin mambobin majalisar suka goyi bayan kudirin dan majalisar.