Labarai
Majalisar yara na yaki da safarar kananan yara
Majalisar yara ta kasa tace majalisar tana yaki da safarar yara zuwa wasu garuruwan da nufin yin aikatau.
Shugabar kwamitin kare hakkin yara ta majalisar Aisha Ayuba Usman ce ta bayyana hakan ta cikin shirin barka da hantsi na nan tashar freedom rediyo da ya mayar da hankali kan irin cin zarafin kananan yara da ake yawan samu a wannan lokacin.
Aisha Ayuba Usman kuma kara da cewa kalubalen da majalisar ke samu a yanzu bai wuce yadda suke samun karancin kai koke ga majalisar ba,duk da cewa ana samun yawaitar cin zarafin kananan yara.
Majalisa ta yanke hukuci ga masu laifi a shafukan sada zumunta
Majalisa ta bukaci hukuncin shekara 5 a gidan yari ga duk malamin da aka kama da cin zarafi
Kai tsaye: An Kammala tantance sunayen kwamishinoni -Majalisar Kano
A nasa bangaren shugaban majalisar yara ta jihar Kano Ameer Mahmud yace iyaye su dinga lura da irin abokanan da yaransu suke mu’amullad dasu.
Da take nata tsokacin mataimakiyar shugaban majalisar yara ta jihar Kano salma umar garo ta ce babbar matsalar da ake samu a yanzu shine yadda iyaye basa jan yaran su a jiki.
Bakin sun karkare da kira ga iyaye dasu dage wajan bawa yaran su ilimi mai inganci domin samun nagartacciyar al umma a nan g