Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Majalisar zartaswar jam’iyyar APC zata daukin matakin kan wa’adin shugabancin jam’iyya

Published

on

Majalisar zartaswar jam’iyyar APC za ta dauki mataki na karshe a ranar Litinin mai zuwa kan maganar karin wa’adin shugabannin jam’iyyar na kasa dana jihohi da ke jagorantar jam’iyyar.

Shugaban jam’iyyar na Kasa Chief John Odigie-Oyegun ne ya bayyana hakan a jiya Laraba bayan wani taron sa’o’i uku da aka gudanar tsakanin gwamnonin jam’iyyar da kuma shugabannin jam’iyyar.

A ranar Talatar da ta gabata ne dai Jam’iyyar ta kaddamar da wani kwamitin mai kunshe da mutane 10 karkashin jagorancin gwamnan jihar Fulato Simon Lalong da su yi duba na tsanaki bisa turka-turkar da ta bullo kan maganar karin wa’adin shugabancin.

Hakan dai yayi dai-dai da matsayar shugaban kasa Muhammadu Buhari kan maganar karin wa’adin, wanda ya ce hakan ya sabawa doka, tare da jawo cece-kuce da rarrabuwar kawuna tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!