Labarai
Majalisar zartaswar Jigawa ta amince da kashe fiye da miliyan 500 don fadada Noman Rani

Majalisar zartarwar jihar Jigawa ta amince da kashe sama da Naira miliyan 500 wajen fadada Noman Rani a Warwade dake yankin karamar hukumar Dutse.
Kwamishinan yada labarai matasa da wasanni Alhaji Sagiru Musa Ahmad ne ya bayyana haka ga manema labarai Jim kadan bayan kammala zaman majalisar zartarwar karkashin jagorancin gwamna Malam Umar Namadi a gidan gwamnatin jihar dake Dutse.
Haka kuma, kwamishinan ya kara da cewa majalisar ta sake amincewa da kudirin sake saka hanun jarin jihar Jigawa a Kamfanin rarraraba wutar Lantarki, KEDCO.
Alhaji Sagiru Musa, ya kuma ce, majalisar ta sake tattaunawa tare da amincewa da kashe sama da Naira miliyan 569 don samar da kayan makaranta wato Uniform ga yara mata dubu 20 a jihar, tare da samar da kujeru a kalla dubu 3,900 a makarantun jihar daban-daban
You must be logged in to post a comment Login