Labarai
Malami: Zamu gurfanar da manyan Najeriya da ake zargi da daukar nauyin ƴan ta’adda
Atoni janar na kasa kuma ministan shari’a Abubakar Malami, ya ce, gwamnatin tarayya ta kammala shirye-shirye don gurfanar da wasu fitattun al’ummar kasar nan gaban kotu wadanda ake zargi suna da hannu wajen tallafawa ayyukan ta’addanci.
Abubakar Malami wanda ke amsa tambayoyin ‘yan jarida a fadar shugaban kasa a jiya juma’a, ya ce, ci gaba da bincike da ake yi kan masu daukar nauyin ayyukan ta’addanci a Najeriya, ya sanya gwamnati ta gamsu da hujjoji da za ta yi amfani da su don gurfanar da wasu fitattun ‘yan Najeriya da ake zargi suna da hannu cikin lamarin.
Ya ce ko a baya-bayan nan jami’an tsaro sun cafke wasu jama’a wadanda ake zargi suna da hannu wajen taimakawa ‘yan ta’dda musamman wadanda ke aiki tare da wasu gungun kungiyoyin da ke samar da kudade ga ‘yan ta’adda a birnin Dubai na hadaddiyar daular larabawa.
You must be logged in to post a comment Login