Kasuwanci
MAN ta bukaci gwamatin tarayya ta janye dokar hana yin kananan Barasa

Kungiyar masu masana’antu na Najeriya MAN, ta buƙaci gwamnatin tarayya da hukumar kula da ingancin abinci da magunguna NAFDAC, da su soke dokar da ta haramta samarwa da sayar da barasa ta Leda da kuma ƙananan kwalabe, wadda ake shirin aiwatarwa daga karshen shekarar nan da muke ciki.
A cewar ƙungiyar, wannan mataki ya zo ne ba tare da cikakken haɗin gwiwa da masu masana’antu ba, kuma ya sabawa matsayar da aka cimma a wani zaman tattaunawa a watan Oktoba da ya gabata.
MAN ta kuma yi gargadin cewa wannan doka ka iya jawo asarar jari da ya kai sama da Naira tiriliyan 1.9, tare da barazanar rasa ayyukan yi ga ma’aikata sama da dubun ɗari biyar.
Masana’antar ta ce ba ta adawa da yunkurin gwamnati na kare lafiyar jama’a, sai dai ta bukaci a sake duba lamarin cikin adalci da haɗin gwiwa domin kaucewa durkusar da masana’antu da kuma ƙaruwar yawan marasa aikin yi a fadin ƙasar nan.
You must be logged in to post a comment Login