Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kimiyya

Mark Zuckerberg ya nemi afuwar al’ummar duniya sakamakon katsewar wasu shafukan sada zumunta

Published

on

Mamallakin kamfanin Facebook da Whatsapp Mark Zuckerberg, ya nemi afuwar al’ummar Duniya sakamakon katsewar shafukan sadarwar a ranar Litinin.

Lamarin dai ya faru kwana guda bayan wata mai bankaɗa da ta taɓa aiki da kamfanin ta fallasa cewa Facebook ya fi fifita ribar da yake hanƙoron samu fiye da kare masu amfani da shafukansa.

Katsewar shafukan ya dakatar da al’ummar Duniya sama da biliyan uku yin  amfani da shafukan.

Cikin kankanin lokaci kamfanin facebook ya yi asarar dala biliyan 7- Mark Zuckerberg

Tuni dai kamfanin ya bayyana cewa ya tafka asarar dala biliyan 7 sakamakon tsayawar manhajojin.

Su ma Masu sharhi na hasashen cewa matsalar da aka samu na katsewar shafukan, na iya janyo wa kamfanin asarar da ta kai ta sama da dala miliyan 3, na harajin talluka.

A ranar Litinin ne dandalin sadarwar na Facebook, WhatsApp da kuma Instagram suka daina aiki na tsawon awanni shida.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!