Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Masarautar Kano ta mayar da wasu dagatai 5 da ta dakatar

Published

on

Majalisar masarautar Kano ta mayar da dagatan nan guda biyar da ke karamar hukumar Kunchi bayan da aka dakatar da su a baya-bayan nan sakamakon wasu laifuka da suka aikata.

Galadiman Kano kuma babban dan majalisar Sarki Alhaji Abbas Sunusi ne ya bayyana hakan yayin zaman majalisar na yau da ya jagoranta.

Alhaji Abbas Sunusi ya ce, mayar da wadannan dagatai ya biyo bayan irin gaskiya da adalci na mai martaba sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi na II akan talakawan sa.

Galadiman Kano ya kara da cewa sarkin na Kano ya kuma gargadi dagatan da su gujewa dukkanin abin da zai jefa su cikin matsala, inda ya ce masarautar kano ba za ta amince da rashin nuna da a ba da wasu ya yan ta ke yi a dukkan matakai.

Cikin dagatan da aka mayar kan mukaman nasu sun hadar da, Danladi Muhammad da Abdullahi Hugungumi da Jamilu Abubakar da Gadaba Abdu Yahya sai Galadimawa Dahiru Muhammad da kuma Ridwan Isyaku Mustapha.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!