Labarai
Masu bukata ta mussaman sun sami tallafi -Dr. Bunkure
Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi ta ce dalibai biyar ‘yan asalin jihar Kano dake fama da lalurar gani suka sami nasarar lashe gasar bada tallafin karatu da wani kamfani mai zaman kansa ya shirya tsakanin makarantun gaba da sakandiran jihohin Arewa maso yamma
Shugaban kwalejin Dr. Yahya Isah Bunkure ya bayyana hakan ne bayan dawowar daliban daga Birnin Tarayya Abuja, yana mai cewa daliban masu lalurar gani sun lashe gasar ne sakamakon kwazon da suka nuna a yayin gasar kuma sun sami kyautar naira miliyan daya su biyar.
Kazalika, shugaban kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi Dr. Yahya Isa Bunkure ya kara da cewa akwai bukatar sauran kamfanoni masu zaman kansu su rika sanya makamanciyar wannan gasa tsakanin dalibai masu bukata ta musamman domin kara musu kaimi a fannin Ilimin su.
Shugaban Tsangayar Ilimin Manya da masu bukata ta musamman Dr. Bala Ladan cewa yayi Allah ya baiwa masu bukata ta musamman baiwa kala-kala don haka ya zama wajibi iyaye su rika kai ‘ya’yan su makarantun masu bukata ta musamman domin bunkasa Ilimin su.
Rabon da mu samu tallafi tun zamanin Malam Ibrahim Shekarau –Masu bukata ta musamman
Rundunar ‘yan sandan jihar katsina ta kama mata hudu dake taimakawa ‘yan ta’adda
Kungiyar dalibai ta Najeriya ta bukaci a rika gina makarantun masu bukata ta musamman
A jawabin daliban su biyar dake fama da matsalar lalurar gani na kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi sun bayyana farin cikin su bisa nasarar da suka samu, inda suka kuma yabawa malaman kwalejin kan irin namijin kokarin su da juriya wajen koyar da su.
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Tukuntawa ya rawaito mana cewa, Sadiya Abdullahi Sanusi ita ce mataimakiyar shugaban tsangayar Ilimin Manyan da Masu bukata ta musamman ta yabawa daliban bisa wannan namijin kokarin da suka yi tare da kira ga sauran kamfanoni masu zaman kan su da su rika kokari wajen daukar su aiki domin tallafawa rayuwar su.
Hajiya Sadiya Abdullahi ta kuma kara da cewa matukar masu bukata ta musamman suka sami abun yi da zasu dogara da kansu shakka babu sunyi bankwana da yawon barace – barace akan tituna wanda ke sanya musu mutuwar zuciya.