Connect with us

Labarai

Masu riƙe da muƙaman siyasa sun sadaukar da rabin albashinsu don yaƙi da ƴan bindiga a jihar Kebbi

Published

on

A wani mataki na taimakawa ƙoƙarin da gwamnatin jihar ke yi don tabbatar da tsaro da lafiyar al’umma, masu rike da mukaman siyasa a jihar Kebbi, sun sadaukar da rabin albashinsu na watan yuni don yaƙi da ƴan bindiga da ke kashe jama’a.

 

Sakataren gwamnatin jihar ta Kebbi, Babale Yauri, shine ya bayyana haka ga manema labarai da yammacin jiya a birnin Kebbi.

 

Ya ce, masu riƙe da mukaman siyasa a jihar sun ɗau wannan mataki ne don taimakawa ƙokarin da jami’an tsaro ke yi wajen daƙile matsalolin tsaro.

 

A cewar sakataren gwamnatin jihar ta Kebbi dai, gwamna Atiku Bagudu da jami’an tsaro suna aiki ba dare ba rana don ganin an kawo ƙarshen hare-haren ƴan bindiga a jihar.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!