Connect with us

Kiwon Lafiya

Mataimakin Gwamnan Kano ya karbi rahotan kwamitin raba tallafin gobarar kasuwannin Kano

Published

on

Gwamnatin jahar Kano ta karbi rahotan kwamitin raba tallafin da aka hada taimakon wadanda gobarar kasuwannin jahar nan suka shafa Karkashin jagorancin mataimakin Gwamnan jahar Kano Farfesa Hafizu Abubakar.

Da yake jawabi lokacin mika rahotan kwamitin Mataimakin Gwamna Farfesa Hafizu Abubakar yace fiye da Naira biliyan daya da kwamitin ya tattara an rabawa yan kasuwa fiye da su dubu 5671  inda Naira miliyan 5 ya rage yana tare da kwamitin  saboda kin zuwa da mutanan suka ki yi suzo su karba duk da cewa an tantance su.

Da yake mai da jawabi Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya godewa kwamitin saboda kokarin da suka yi sannan ya tabbatarwa da Yankasuwar cewa Gwamnatinsa tare da hadin gwiwar Gwamnatin tarayya zasu saka wutar lantarki mai amfani da rana a kowanne shago a kasuwannin sabongari  da na kwari domin su yi gogayya da sauran kasuwanni a Duniya.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,340 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!