Connect with us

Manyan Labarai

Matar da ta makance sakamakon kashe ‘’yayanta sojoji biyu ta samu taimako ta kafar sada zumunta

Published

on

Aisha Umar uwa ce ga sojoji guda biyu Abubakar Hassan da Mubarak Hassan dake yaki da yan tayar da kayar baya a birnin Maiduguri na jihar Borno.

Aisha ta rasa ‘yayanta sakamakon yaki da yan Boko Haram a yankin.

Dalilin haka da kuma yawan damuwa ya saka Aisha ta makance sakamakon hawan jini da ya saka ta ciwon ido .

Idonta na farko ne ya fara makancewa sannan dayan ya kamu.

Ganin haka ne lauyan nan mai kare hakkin dan Adam Barrister Audu Bulama Bukarti da daya lauyan dan gwagwarmaya Barrister Abba Hikima suka fara neman taimako ta kafar sadarwa dan tarawa wannan mata taimako .

A lokacin da muka hada wannan labari wannan baiwar Allah ta samu taimakon kimanin Naira dubu  dari da ashirin da tara domin ta cigaba da neman maganin idanun nata.

Audu Bulama Bukarti yace har yanzu kofa a bude take ga masu san taimakawa wannan mata ta bankin FCMB mai dauke da lambar account kamar haka, 0514907018 sunan account din kuma  ABBA AMINU HIKIMA.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 334,958 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!